Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan harkokin kimiyya da fasaha: Sin za ta habaka hadin gwiwar kimiyya da fasaha
2020-10-30 14:53:41        cri
A yayin taron manema labarai game da cikakken zama na 5, na kwamitin tsakiya na 19 na JKS da aka yi a yau Jumma'a, ministan harkokin kimiyya da fasaha Wang Zhigang ya bayyana cewa, bunkasuwar kimiyya da fasaha, ba ta saba wa ka'idar karfafa hadin gwiwa a tsakanin bangarori daban daban ba, a nan gaba kuma, kasar Sin za ta karfafa aikin habaka hadin gwiwa a fannin kimiyya da fasaha.

Wang ya kara da cewa, gabanin sauye-sauyen yanayi cikin kasar Sin da ma kasashen duniya, ya kamata kasar Sin ta aiwatar da sabbin ra'ayoyin neman ci gaba, da inganta bunkasuwar kasa mai inganci, da kafa sabon tsarin neman ci gaban kasa, sabo da haka, tana matukar bukatar raya harkokin kimiyya da fasaha, domin fitar da wasu sabbin dabarun raya kasa.

Ya ce a nan gaba, Sin za ta yi kirkire-kirkire, da kwaskwarima, domin raya harkokin kimiyya da fasaha, da inganta tattalin arziki, da biyan bukatun kasa, da kuma kiyaye lafiyar al'umma. Za ta kuma karfafa ayyukan kimiyya da fasaha bisa manyan tsare-tsare, ta yadda za ta habaka ayyukan kirkire-kirkire yadda ya kamata, yayin da take gina wata kasa mai ci gaba a fannin kimiyya da fasaha. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China