Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta fito da matakai hudu na samun dogaro da kai a fannin kimiya da fasaha
2020-11-04 11:30:38        cri
Kwamitin koli na JKS dake fasalta shirin raya tattalin arzikin da rayuwar al'ummar Sinawa na shekaru biyar karo na 14, da manufofi na dogon zango da ake fatan cimmawa nan da shekarar 2035, ya sanar a jiya Talata cewa, kirkire-kirkire shi ne jigon shirin zamanantar da kasar Sin. A don haka, idan har kasar Sin tana son cimma wannan buri, wajibi ne ta dogara da kanta a fannin kimiya da fasaha, ta yadda za ta tunkari ci gaban kimiya da fasaha na duniya, da matsalar tattalin arziki, da manyan bukatun kasa da lafiya da rayuwar al'umma, da kara aiwatar da matakan farfado da kasa ta hanyar kimiya da Ilimi, da kara karfin kasa ta hanyar amfani da masana da bunkasa kirkire-kirkire, da inganta tsarin kirkire-kirkire, don kara karfin kimiya da fasahar kasar.

Daga cikin manyan ayyuka 12 da aka gabatar wajen tsara shirin, abu na farko shi ne, a nace ga raya kirkire-kirkire, a kuma dunkule sabbin nasarorin da aka cimma. Shirin ya kunshi fannoni guda hudu, Na farko karfafa dabarun kasa na raya kimiya da fasaha, da kara karfin kamfanoni a fannin kirkire-kirkire, da karfafa gwiwar masu basirar kirkire-kirkire da inganta tsari da matakan kirkire-kirkire na kimiya da fasaha.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China