Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta kara zage damtse wajen dorewar farfadowar tattalin arzikin duniya
2020-10-30 20:48:54        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a yau Jumma'a cewa, duba da yadda aka tsara gami da aiwatar da shirin raya tattalin arziki da kyautata rayuwar al'umma na shekaru biyar karo na 14 da babban burin da aka sanya gaba zuwa shekara ta 2035, Sin za ta kara zage damtse wajen habaka tattalin arzikin duniya cikin dogon lokaci.

Kwanan nan, akwai shugabannin kasashe da dama, gami da cibiyoyin kudi da manyan kamfanonin kasa da kasa wadanda suka bayyana kyakkyawan fatansu ga makomar tattalin arzikin kasar Sin, inda suke da yakini da ma fatan alheri ga makomar bunkasuwar kasar. Mista Wang ya ce, sanarwar bayan taron cikakken zama na biyar na kwamitin koli na JKS na 19 da aka fitar ta yi nuni da cewa, karfin kasar Sin ya kai wani sabon matsayi, wadda za ta tsaya tsayin daka kan ra'ayin samar da ci gaba ta hanyar kirkire-kirkire, da kara bude kofarta ga kasashen ketare don bullo da sabbin damammaki na hadin gwiwa da juna. Haka kuma kasar Sin za ta gaggauta kafa wani sabon tsarin samar da ci gaba, wato idan aka mayar da hankali kan raya tattalin ariki a cikin gida, za'a iya hade kasuwar cikin gida da ta ketare domin samun ci gaba mai karfi da dorewa, ta yadda kasar Sin za ta yi kokarin zamanantar da tsarin gurguzu nan da shekara ta 2035.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China