Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Reuters: Bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ta ingiza farfadowar nahiyar Asiya
2020-11-02 10:50:40        cri

Reuters ta ba da labari kwanakin baya cewa, tattalin arzikin nahiyar Asiya na da alamar farfadowa duba da damammakin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin. Kusan shekara daya bayan bullar cutar COVID-19 a duniya, Sin tana shiga wani sabon mataki na samun bunkasuwa.

Labarin ya ce, kasashen duniya na mai da hankali matuka kan babban zaben Amurka dake tafe da kokarin da nahiyar Amurka da Turai ke yi na hana yaduwar cutar, a wani bangare kuma, Sin ta samu ci gaba mai armashi a fannoni daban-daban.

Bayan matakin kulle mai tsanani da Sin ta dauka a farkon barkewar cutar, Sin ta zama kasa daya kacal a cikin hasashen da IMF ta yi na samun karuwar tattalin arziki a duniya bana.

Alkaluman da aka bayar na nuna cewa, karuwar tattalin arzikin kasar Sin a rubu'i na 3 ya kai kashi 4.9%, adadin ya kai kashi 3.2% a rubu'i na 2. Amma, a lokacin da cutar ta fi kamari a farkon wannan shekara, adadi ya ragu da kashi 6.8%.

Manazarin harkokin tattalin arziki na bankin Westpac na Austriliya ya nuna cewa, bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a wannan mataki na da karfi na dogon lokaci. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China