Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Birtaniya ta daga matakin barazanar ta'addanci zuwa mafi tsanani, bayan harin da aka kai Vienna
2020-11-04 10:28:14        cri
Birtaniya ta daga matakin barazanar ta'addanci a kasar zuwa mafi tsanani a jiya Talata, wanda ke nufin akwai yuwuwar aukuwar harin ta'addanci.

Kafar yada labarai ta Sky ta bada rahoton cewa, cibiyar nazarin ayyukan ta'addanci ta hadin gwiwa ta JTAC, wadda ke karkashin hukumar tsaro ta MI5 ce ta yanke shawarar daga matakin.

Sakatariyar kula da harkokin cikin gidan kasar, Priti Patel, ta bayyana matakin a matsayin na kandagarki, tana mai cewa, bai dogara da wata takamammiyar barazana ba.

Ta yi kira ga jama'a su ci gaba da sa ido da kai rahoton duk wani abu da ba su yadda da shi ba ga 'yan sanda.

Wannan na zuwa ne bayan a ranar Litinin, wani da ake zargin dan ta'adda ne ya harbe wasu mutane 4 har lahira, a birnin Vienna na Austria. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China