Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Birtaniya ya harbu da cutar COVID-19
2020-03-27 21:02:25        cri
Kakakin Firaministan Birtaniya, ya ce sakamakon bincike da aka gudanar, ya nuna cewa firaminista Boris Johnson, ya harbu da cutar numfashi ta COVID-19. Jami'in ya ce firaminista Johnson ya fara nuna wasu kananan alamu na kamuwa daga cutar, ya kuma kebe kan sa a fadar gwamnati ta Downing Street.

Shi ma firaministan da kan sa, ya aike da wani sako ta Twitter, yana mai tabbatar da hakan. Ya ce "Zan ci gaba da gudanar da ayyukan hukuma ta kafar bidiyo, yayin da muke ci gaba da yaki da wannan annoba."

Kawo yanzu dai adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a Birtaniya sun haura mutum 11,600, kuma tuni cutar ta hallaka mutane sama da 570 a kasar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China