Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jarida: Bai Dace Birtaniya Ta Zama 'Yar Amshin Shatan Amurka Ba
2020-08-18 11:24:50        cri

A kwanan baya, jaridar Morning Star ta kasar Birtaniya, ta ruwaito shahaharren mai tsara fim na kasar John Pilger, na cewa ya kamata kasar Birtaniya ta yi taka tsan-tsan yayin da take hadin gwiwa da kasar Amurka a fannin hulda da kasar Sin, don kaucewa zama 'yar amshin shatan Amurka.

A cewar Johon Pilger, dalilin da ya sa kasar Amurka ke kokarin matsawa kasar Sin lamba, shi ne tana son kare matsayinta na kasa daya tak dake da matukar karfi a duniya.

Pilger ya ce akwai kalamai na suka da wasu 'yan siyasa da kwararru na kasar Amurka suke yi wa kasar Sin, kan yadda kasar take kalubalantar yammacin duniya, inda take girgiza fifiko da hakkin da suke samu. Sa'an nan gwamnatin kasar Amurka tana rufawa masu yayata irin wadannan kalamai baya, don su ci gaba da shafa kashin kaji ga kasar Sin.

A cewar mista Pilger, ya kamata a yi watsi da zargin da wasu kafofin labaru suke yi wa kasar Sin, cewa wai tana danne makwabtanta. Hakika wadannan kafofin watsa labaru ba su da wata magana da za su iya fada, ban da kalmomi marasa dadi game da kasar Sin.

Jaridar Morning Star ta kara da cewa, babbar manufar kasar Amurka a fannin hulda da sauran kasashe, ita ce kare damarta ta yin babakere a duniya, da karfafa tsarin kasa da kasa da ya shafi tattalin arziki, da diplomasiyya, da al'adu, da kuma aikin soja, wanda zai taimakawa tabbatar da moriyar masu hannu da shuni na kasar Amurka. Wannan manufa ta sa kasar kunna wutar yake-yake a kasashen da suka hada da Iraki, da Libya, da Syria, da Afghanistan da dai sauransu.

Yayin da a hannu guda kasar Sin, a cewar mista Pilger, take neman ingiza hadin gwiwar da kasa da kasa cikin lumana, da yin takara amma ba tare da samun rikici ba. Kasar ta ki goyon bayan haifar da yake-yake, maimakon haka tana neman samun hadin kan bangarori daban daban masu fada a ji a duniya. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China