Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masaniyar Birtaniya: Kasar Birtaniya za ta dandana kudar katse huldar ciniki tsakaninta da kasar Sin
2020-07-24 13:17:50        cri

Kwanan baya, jaridar Financial Times ta kasar Birtaniya ta wallafa wani bayanin da Carolyn Fairbairn, babbar daraktar kungiyar kawancen sha'anin masana'antu na kasar wato CBI ta rubuta, mai taken "Kasar Birtaniya za ta dandana kudar katse huldar ciniki tsakaninta da kasar Sin". Bayanin ya nuna cewa, cinikayyar kasashen biyu na da babbar ma'ana ga kasar Birtaniya, kuma yanzu kasar na fuskantar mawuyancin hali na yakar cutar COVID-19 da rashin aikin yi, idan ta yanke shawarar katse huldar ciniki da kasar Sin, kasar ba za ta iya jure wannan sakamako ba ko kadan. A cewar bayanin, kamata ya yi gwamnatin kasar ta kimanta asarar da za ta yi kafin ta katse huldarta da kasar Sin ta fuskar ciniki, sannan ta yi hangen nesa ta kafa dangantaka mai kyau da kasar Sin a wannan fanni.

A ranar 14 ga wata, kasar Birtaniya ta sanar da hana duk kamfanoninta na sadarwa amfani da na'urorin kamfanin Huawei kan fasahar intanet ta 5G a kasar, bisa dalilin tsaron kasar, har ma ta ce za a yi watsi da duk wata na'urar Huawei kafin shekarar 2027.

Carolyn Fairbairn ta kuma yi kira da a gabatar da wani shiri na daban da ya samu amincewa daga bangarori daban-daban kafin a hana shigar da kayayyaki daga kamfanonin kasar Sin ciki hadda Huawei bisa dalilin tsaron kasar, idan ba haka ba, kasar za ta dandana kudarta bisa daukar matakin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China