Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bukaci majalisar wakilan Burtaniya da ta daina bata mata suna
2020-04-09 13:00:44        cri

Kakakin ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Burtaniya a jiya Laraba ya bukaci kwamitin kula da harkokin waje na majalisar wakilan kasar da ya yi watsi da ra'ayin yakin cacar baki da daina bata sunan kasar Sin, da nuna adalci bisa hakikanin halin da ake ciki kan kokarin da kasar Sin ke yi da nasarar da ta cimma wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19, ta yadda za ta taka rawa a hadin kan dake tsakanin kasashen biyu a wannan fannin da kuma kare lafiyar al'ummar duniya baki daya.

A ranar 6 ga wata ne, kwamitin kula da harkokin waje na majalisar wakilan kasar Burtaniya ya bayar da rahoto game da yanayin annobar cutar COVID-19, inda ya yi fatali da namijin kokarin da Sin ke yi da ma gudummowar da ta bayar yayin da ake yaki da annobar a duniya, har ma ya shafa wa kasar Sin kashin kaji cewa, wai kasar ta boye yanayin annobar, da sanar da labaru da ba na gaskiya ba. Ban da wannan kuma kwamitin ya mai da kasar Sin a matsayin wurin da cutar da samo asali ba tare da wata hujja ba.

Kakakin ofishin jakadancin kasar Sin dake Burtaniya ya bayyana cewa, sanin asalin cuta batu ne na kimiyya mai sarkakiya da wahalar sha'ani, masana da kwararru a wannan fannin ne kadai za su iya yin bayani bisa kwararan shaidu.

Baya ga haka, kakakin ya jaddada cewa, cutar ba ta san kasa ko kabila ba, kuma abokin gaban daukacin bil Adama ne. A cikin wannan lokacin mai muhimmanci, kamata ya yi kasashe daban daban su yi la'akari da halin da duniya ke ciki da yin hangen nesa, kuma su hada kai don tinkarar wannan mawuyacin hali. Ya kara da cewa, kasar Sin tana adawa da duk mai neman fakewa da annobar wajen sanya batun siyasa, da haddasa sabani da kawo baraka a tsakanin kasashe daban daban, hakan ba abin da zai kawo sai cikas ga hadin kai a tsakanin kasa da kasa wajen yakar cutar.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China