Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Burtaniya da Faransa sun yi hasashe cewa, tattalin arziki zai ragu
2020-03-25 13:05:34        cri
Jiya Talata, kamfanin samar da labaran kididdiga ga birnin London na kasar Burtaniya, wato IHS Markit, ya fidda rahoto cewa, barkewar cutar numfashi ta COVID-19 ta kawo asara matuka ga sana'ar ba da hidima, lamarin da ya sa, kasar Burtaniya ke fuskantar saurin raguwar tattalin arziki, wadda ba ta taba gamuwa da ita cikin shekaru 20 da suka gabata ba. Kamfanin ya ce, bai taba fidda rahoto maras kyau kamar haka ba tun daga shekarar 1998 da ya fara tsara irin wannan rahoto.

Haka kuma, cikin rahoton, an ce, cikin watanni da dama masu zuwa, mai yiyuwa, tattalin arzikin kasar Burtaniya zai tsaya gaba daya bisa ci gaban matakan da za ta dauka domin dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, kamar kasawar kamfanoni da dai sauransu. Lamarin zai kasance kasawar da ba a taba ganin irinsa ba cikin zamani.

Haka kuma, cikin taron manema labaran da aka yi a jiya Talata, ministan kula da harkokin tattalin arzikin kasar Faransa Bruno Le Maire ya bayyana cewa, yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 ta kawo asara matuka ga tattalin arzikin da ba na yanar gizo ba, a nan gaba kuma, za ta kawo asara ga sauran ayyukan da abin ya shafa. Ya ce, ba a taba gamuwa da irin wannan asarar tattalin arziki ba, tun bayan babbar faduwar tattalin arziki a shekarar 1929. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China