2020-10-21 14:26:30 cri |
Wani rahoton MDD da aka wallafa a ranar Talata ya nuna cewa, halayyar dukan matan aure ya yi matukar kamari a kasashen Afrika, Asiya, da yankin Oceania, amma ban da kasashen Australia da New Zealand, kana ana samun karancin matsalar a kasashen Latin Amurka da yankin Karibbean da Turai.
Ana samun raguwar cin zarafin a tsakanin ma'aurata. A cikin shekaru 8 wato daga shekarar 2012 zuwa 2019, an samu raguwar cin zarafin mata daga wajen mazajensu da kusan kashi 75 bisa 100 a kasashen kamar yadda alkaluman suka nuna, a cewar kididdigar mata ta 2020, inda aka tattara bayanan labarai 100 wanda aka dauki hotunan yanayin daidaito a tsakanin jinsi da aka samu a fadin duniya.
Sashen kula da alkaluman kididdigar tattalin arziki da kyautata rayuwar al'umma na MDD ya samar da rahoton na matan duniya wanda ake fitarwa a duk bayan shekaru biyar, kuma an fara samar da rahoton ne tun a shekarar 1990, kana an samar da sabbin alkaluma na baya bayan nan game da yanayin daidaiton jinsi a duniya.(Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China