Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AUļ¼šAna kara damawa da matan Afirka a harkokin siyasa
2020-10-19 09:25:18        cri
Hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka (AU) ta bayyana cewa, ana kara samun mata a nahiyar Afirka da ake damawa da su a harkokin siyasa a cikin shekaru goma da suka gabata.

Kungiyar mai mambobi 55 ta ba da misali da kasashen kungiyar guda hudu, da suka kasance cikin kasashe goma na farko a duniya, wadanda ke da yawan wakilai mata a majalisun dokokin kasashensu. Wadannan kasashe su ne Rwanda, da Namibia, da Afirka ta Kudu da kuma kasar Senegal.

Bugu da kari, wasu karin kasashe da yankuna 16 dake nahiyar, sun dara kaso 30 cikin 100 na yawan wakilai mata a majalisun dokokinsu. A cewar kungiyar ta AU, yanzu haka akwai mata dake rike da muhimman ma'aikatu, kamar na tsaro, da tattalin arziki, da harkokin kudi da harkokin waje, wadanda a baya bisa al'ada a maza ake baiwa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China