Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gudanar da bincike zai taimakawa kokarin Afirka na aiwatar da AfCFTA
2020-10-21 10:30:02        cri

Hukumar MDD mai kula da harkokin tattalin arzikin nahiyar Afirka (UNECA) ta jaddada cewa, ci gaba da gudanar da bincike, shi ne babban jigon da zai taimakawa kokarin nahiyar Afirka na aiwatar da yankin cinikayya maras shige na nahiyar wato AfCFTA a takaice.

Hasashen hukumar ta ECA na baya-bayan nan na nuna cewa, nan da shekarar 2040, yankin cinikayyar nahiyar na AfCFTA, zai kara yawan kayayyakin abinci da amfanin gona da yake fitarwa zuwa dala miliyan 16.8. Fannonin makamashi da hakar ma'adinai kuma zai kai dala biliyan 9, yayin da kayayyyakin masana'antun da za a fitar zai kai darajar dala biliyan 43.3

Shi ma babban darektan sashen cinikaya da dunkulewar shiyya na hukumar ECA Stephen Karingi, ya jaddada cewa, yankin cinikayyar nahiyar maras shinge, ya kara samar da damammaki na kasuwanci a sassan nahiyar, da Karin hanyoyin samun kudaden haraji ga gwamnatoci, sakamakon karuwa da sabbin damammaki na kasuwanci.

Sai dai ya ce, nasarar aiwatar da yarjejeniyar, ta dogara kan hukumomin tattalin arziki dake shiyyar, da yadda aka yi amfani da nasarorin da shiyyoyin harkokin tattalin arziki suka cimma, da yadda za a kaucewa fadawa wasu matsaloli da kalubale da suka fuskanta a baya.

Darektan hukumar ya bayyana haka ne, yayin taron shekara-shekara na dandalin kasuwar bai daya ta kasashen gabashi da kudancin Afirka karo na 7 (COMESA), mai taken "Cin gajiyar cinikkayya tsakanin kasashe mambobin COMESA, ta hanyar yarjejeniyar AfCFTA.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China