Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yarjejeniyar AfCFTA za ta taimaka ga bunkasar tattalin arzikin Afirka
2019-07-16 10:49:11        cri
Ministan kasuwanci da masana'antu na kasar Afirka ta Kudu Ebrahim Patel ya bayyana cewa, yarjejeniyar cinikayya maras shige ta Afirka ko AfCFTA a takaice za ta kara bunkasa harkokin tattalin arziki da cinikayyar kasar, kana wata kafa ce ta bunkasa tattalin arzikin nahiyar baki daya.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake bayani game da yarjejeniyar. Yana mai cewa, yarjejeniyar za ta taimakawa bangaren masana'antu duba da yadda za a rika sayar da kayayyakin da suke sarrafawa a kasuwa mai yawan al'umma biliyan 1.2.

Patel ya ce, yarjejeniyar za kuma ta canja tare da sake fasalin tattalin arzikin kasar Afirka ta Kudu. Ya ce tuni ma, kayayyakin da kasar take fitarwa zuwa sauran kasashen nahiyar, suka samar da ayyukan yi kimanin 250,000 a kasar, inda ya kasance bangare mafi saurin bunkasa a kasar.

Ya kuma yi nuni da cewa, shirin zai gina wani harsashin karuwar cinikayya tsakanin kasashen nahiyar tare da karfafa matsayin nahiyar a matsayin yankin da zai bunkasa nan gaba.

Sai dai ya ce, akwai bukatar a tsara matakan da suka dace, idan har ana son cin gajiyar yarjejeniyar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China