Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ghana za ta bada gudunmuwar dala miliyan 10 na kaddamar da aikin sakatariyar AfCFTA
2019-07-08 11:22:14        cri

Shugaban kasar Ghana Nana Dankwa Akufo Addo, ya yi alkawarin bada gudunmuwar dala miliyan 10 ga Tarayyar Afrika, domin taimakawa wajen kaddamar da sakatariyar yankin ciniki mara shinge na nahiyar Afrika.

Taro na 12 na shugbanannin kasashe mambobin AU da aka yi jiya a Niamey na Niger ne ya zabi Ghana a matsayin kasa mai masaukin yankin na ciniki maras shinge, bayan ta yi nasara kan kasashe 6 ciki har da Masar da Habasha a takarar da aka yi.

A jawabin da ya yi, shugaban ya godewa taron, yana mai cewa dama ce a karon farko ga tarihin kasar, na daukar nauyin bada masauki ga cibiyar mai muhimmanci ga nahiyar Afrika.

Ya bada tabbacin Ghana za ta sanya abubuwan da ake bukata a sakatariyar ta yadda za ta yi aiki a matsayin ta kasa da kasa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China