Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta bukaci a karfafa hadin gwiwa domin cimma burin yarjejeniyar ciniki mara shinge ta Afrika
2019-09-26 11:28:09        cri
Hukumar kula da tattalin arzikin nahiyar Afrika ta MDD, UN-ECA, ta jaddada bukatar karfafa hadin gwiwa domin cimma nasarar yarjejeniyar kafa yankin ciniki cikin 'yanci ta nahiyar.

Hukumar ECA wadda ta bayyana hadin gwiwarta da hukumar raya cinikayya a yankin gabashin Afrika TMEA, wadda ke da nufin tabbatar da yarjejeniyar na aiki yadda ya kamata ga mata da matasa, ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya.

Daraktan ofishin hukumar ECA a gabashin Afrika, Andrew Mold, ya yabawa hadin gwiwar hukumomin ECA da TMEA, yana mai cewa hadin gwiwa tsakanin ECA da TMEA da hukumar kula da ayyukan Tarayyar Afrika da hukumar raya ciniki da ci gaba ta MDD UNCTAD da sauransu, shi ne tubalin da zai ingiza ajandar dunkulewar nahiyar.

Hukumar ECA, wadda take ta goyon bayan tabbatar da yarjejeniyar ciniki mara shinge ta Afrika, a matsayinta na babbar mai yunkurin samar da kasuwar bai daya a nahiyar, ta kuma jaddada bukatar wayar da kan al'umma game da ba mata da bukatunsu muhimmanci ta hanyar samar da kasuwa guda daya ta nahiyar, kamar yadda yarjejeniyar ta tanada.

Andrew Mold ya nanata bukatar kara wayar da kai game da yarjejeniyar a tsakanin kungiyoyin mata da matasa da kamfanoni masu zaman kansu, yana mai cewa, ilmantar da al'umma game da yarjejeniyar, zai taimaka wajen kawar da rashin fahimta. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China