Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU za ta ci gaba da gudanar da ayyukan kaddamar yarjejeniyar AfCFTA ta hanyar amfani da fasahar zamani yayin da ake fama da COVID-19
2020-08-19 10:38:24        cri

Yayin da ake sa ran yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci ta nahiyar Afrika za ta fara aiki a ranar 1 ga watan Junairun 2021, Tarayyar Afrika ta ce za ta ci gaba da gudanar da harkokin da suka shafi aiwatar da yarjejeniyar ta hanyoyin fasahar zamani yayin da ake fama da COVID-19.

Wata sanarwa da Tarayyar ta fitar a jiya, ta ce idan ana son cimma lokacin da aka sanya na fara aiwatar da yarjejeniyar, kuma ana son aiwatar da matakin da shugabannin nahiyar suka dauka da nufin gaggauta ayyukan da za su kai ga kaddamar da yarjejeniyar, to dole ne a ci gaba da tattaunawa ta kafar intanet.

An mika ayyuka tare da kaddamar da ginin sakatariyar yankin cinikayyar ne ranar Litinin, a birnin Accra na Ghana.

Hukumar kula da ayyukan AU ta bayyana fatan fasahohin zamani za su taka rawa gaya wajen ingiza hadin gwiwa tsakanin kasashen mambobi domin tabbatar da ayyuka sun gudana cikin aminci.

A don haka, an kara fadada ayyukan kwamitocin kwararru, ta yadda za su kunshi sake nazarin damarmakin dake akwai ga mambobi, ciki har da na fasahohin zamani, wadanda za a iya amfani da su wajen gabatar da cinikayya karkashin yarjejeniyar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China