Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yarjejeniyar AfCTFA za ta bunkasa ingancin kayayyakin da Nijeriya ke fitarwa waje
2019-11-27 09:45:01        cri

Yarjejeniyar kafa yankin ciniki cikin 'yanci ta nahiyar Afrika, wadda kashinta na farko ya fara aiki a watan Yuli, ya samar da dama ga Nijeriya, ta kara ingancin kayayyakin da ake sarrafawa a kasar tare da fitar da su waje.

Cikin wata sanarwa da aka fitar, Ministan kula da masana'antu da cinikayya da zuba jari na kasar, Niyi Adebayo, ya ce masu sarrafa kayayyaki a Nijeriya na da damar kara ingancin kayayyakinsu da za a fitar zuwa fadin nahiyar bisa aiwatar da yarjejeniyar.

Ya ce gwamnatin Nijeriya ta kuduri niyyar warware duk matsalolin dake tarnaki ga yanayin kasuwanci, kuma hukumomin masu ruwa da tsaki na aiwatar da shirye-shirye daban-daban da za su ba kamfanonin kasar damar cin gajiyar yarjejeniyar.

A cewarsa, idan nahiyar na son cimma karfinta na baza koma da sauya fasalin tattalin arziki ta hanyar yarjejeniyar AfCTA, to dole ta yi aiwatar da dabarun fitar da kayayyaki da baza komar tattalin arziki da bunkasa masana'antu da kuma raya harkar samar da kayayyaki. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China