Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Boss Mustapha: Masu zanga zanga na iya habaka yaduwar COVID-19 a Najeriya
2020-10-20 19:58:56        cri
Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya Boss Mustapha, ya ce akwai hasashen karuwar masu harbuwa da cutar numfashi ta COVID-19 a sassan kasar, sakamakon yadda dubban jama'a masu zanga-zanga ke cakuduwa da juna, ba tare da kiyaye ka'idojin kaucewa harbuwa da cutar ba.

Boss Mustapha ya ce, cikin makwanni biyu masu zuwa, mai yiwuwa za a samu karin masu harbuwa da COVID-19, duba da yadda masu zanga zangar kin jinin cin zalin da 'yan sandan rundunar SARS ke yiwa al'umma, ke ci gaba da yin jerin gwano a sassan kasar daban daban.

Sakataren gwamnatin Najeriyar, wanda shi ne kuma shugaban kwamitin ko ta kwana na shugaban kasar game da yaki da cutar, ya bayyana hakan ne yayin wata zantawa da manema labarai yau a birnin Abuja, fadar mulkin kasar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China