Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin wadanda suka kamu da COVID-19 a Nijeriya ya kai 442
2020-04-17 10:13:47        cri
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka da kandagarkinsu ta Nijeriya, NCDC, ta ce adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a kasar ya karu zuwa 442, inda aka samu sabbin mutane 35 da aka tabbatar sun kamu da cutar a jiya Alhamis.

Cibiyar ta ce an kuma samu mutum guda da ya mutu a jiyan, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu sanadiyyar cutar a kasar, zuwa 13.

Sanarwa da cibiyar ta fita, ta ruwaito cewa, kawo yanzu akwai mutane 152 da aka sallama daga asibiti bayan sun warke.

A ranar Litinin ne Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya sanar da tsawaita dokar hana fita a jihohin Lagos, da Ogun, da babban birnin kasar Abuja, da karin makonnin 2, yana mai cewa matakin shi ne hanya mafi dacewa ta dakile yaduwar cutar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China