Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a dawo da zirga-zirga jiragen saman kasashen waje a Nijeriya
2020-08-18 11:11:08        cri

Bayan shafe watanni da dakatar da zirga-zirgar jiragen saman kasashen waje, Ministan kula da sufurin jiragen sama na Nijeriya, Hadi Sirika, ya sanar da cewa, za a dawo da zirga-zirgar jiragen a ranar 29 ga wata.

A cewar Hadi Sirika, dawowar zirga-zirgar jiragen kasashen wajen, za ta gudana ne kamar yadda aka yi na cikin gida.

Ministan ya bukaci al'ummar kasar su yi hakuri da matakin dakatarwar da ake ciki, yana mai cewa za a sanar da ka'idojin dawo da zirga-zirgar jiragen a lokacin da ya dace. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China