Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a gudanar da bikin makon cinikayyar Sin da Afirka ta bidiyo a karshen watan Yuni
2020-06-23 11:05:44        cri

Mashirya bikin makon cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashen nahiyar Afirka, sun tabbatar da cewa, a bana za a gudanar da ayyukan makon ne ta kafar bidiyo, tsakanin renekun 29 ga watan nan na Yuni, zuwa 5 ga watan Yuli, inda ake sa ran nuna salon cinikayya mai armashi dake wanzuwa tsakanin sassan biyu, duk kuwa da irin kalubale da cutar numfashi ta COVID-19 ta haifar ga fannin.

Mashirya bikin, sun ce akwai jami'an gwamnatoci, da masu zuba jari, da masu baje kolin hajoji na Sin da na kasashen Afirka, da za su shiga a dama da su a ayyukan makon na bana ta kafar sadarwar zamani.

Cikin wata sanarwa da mashirya shirin ko MIE suka fitar a birnin Nairobin kasar Kenya, ana sa ran masu baje hajoji sama da 1,000 za su shiga a dama da su a bikin na bana, ta wani dandalin yanar gizo mai lakabin "Global Trade Week" ko GTW a takaice.

An ce ta dandalin na GTW, masu halartar bikin za su samu damar binciko shafukan masu sarrafa hajoji, da kayayyakin da ake samarwa ta yanar gizo, za su kuma iya tattaunawa da masu sayar da kayayyaki kai tsaye, har ma su tsara gudanar da taro, da tattaunawar karawa juna sani ta bidiyo ba tare da wata matsala ba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China