Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya ce a shirye yake ya tabbatar da kyautatuwar dangantakar Sin da Equatorial Guinea
2020-10-15 09:25:00        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce a shirye yake ya yi aiki tare da takwaransa na kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo wajen amfani da bikin cika shekaru 50 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu a matsayin wata muhimmiyar damar ingiza dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa sabon mataki.

Xi ya yi wannan tsokaci ne a sakon taya murnar da suka aikewa juna, inda ya bukaci bangarorin biyu da su martaba dangantakar siyasar a tsakaninsu, kana su zurfafa hadin gwiwarsu karkashin shawarar ziri daya da hanya daya da dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika FOCAC.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China