Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya bayyana sirrin Shenzhen na sauyawa daga karamin kauye zuwa babban birni
2020-10-14 19:13:27        cri

Shenzhen a Sinanci na nufin kwalbati mai zurfi a filin gonaki. Kafin shekaru 40 da suka gabata, Shenzhen wani karamin kauye ne mai fama da talauci da ke kusa da teku.

A shekarar 1980, Shenzhen ya zama daya daga cikin yankunan musamman na tattalin arziki da kasar Sin ta fara bude kofarsu ga ketare, lamarin da ya sa wurin fara aiwatar da manufar kasar Sin ta bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida.

A cikin shekaru 40 da suka gabata, an ga abubuwa na ban al'ajabi da suka faru a birnin Shenzhen sakamakon saurin ci gabansa.

Yau birnin Shenzhen ke cika shekaru 40 da zama yankin tattalin arziki na musamman, an kuma shirya gagarumin biki a birnin, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana sirrin ci gaban Shenzhen.

Tsarin Shenzhen: Yaya aka haifar da al'ajabi a Shenzhen?

A kan ce, "An gina hawa daya na gini a cikin kwanaki uku", maganar ta shaida saurin gina birnin Shenzhen. Don haka, an gina birnin Shenzhen daga kauyen kamun kifi mai talauci zuwa birni mai ci gaba, kana an haifar da tsarin Shenzhen. A gun bikin murnar cika shekaru 40 da kafa yankin tattalin arziki na musamman na Shenzhen, shugaba Xi Jinping ya bayyana fasahohi 10 na tsarin Shenzhen, wato nacewa kan manufar gina yankin bisa jagorancin jam'iyyar kwaminis ta Sin, da kyautata tsarin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin, da dora muhimmanci kan samun ci gaba, da yin kwaskwarima, da bude kofa ga kasashen waje a dukkan fannoni, da yin kirkire-kirkire don zama matsayin gaba a yayin da ake samun babban canji kan kimiyya da fasaha da sana'o'i a duniya, da kiyaye tunanin samun bunkasuwa bisa tushen jama'a don kara amfanawa jama'a cikin adalci.

A farkon shekarun 1980 na karnin da ya gabata, aka gina yankin masana'antu na Shekou dake birnin Shenzhen, wanda ya kasance yanki na farko da ya bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin.

A unguwar CBD dake birnin Shenzhen a halin yanzu, babban ginin cibiyar hada-hadar kudi ta kasa da kasa ta Ping'an dake da tsayin mita 599.1 ya kasance sabuwar alama ta birnin Shenzhen.

Ruhin Shenzhen, shi ne sirrin da birnin yake da shi wajen samar da abin al'ajabi

Shekaru 40 da suka wuce, Shenzhen, ya kasance wani karamin gari mai fama da koma baya da ke yankin karkara, amma yanzu ya kasance matsayin babban birnin kasa da kasa wanda ke yin gagarumin tasiri a duniya. Wasu shahararrun kamfanonin fasahar zamani na kasar Sin kamar Huawei, Tencent, da DJI sun kafa babban zaurensu a Shenzhen. Mutane fiye da miliyan 13 suna kokarin cimma burinsu a wannan birni mai kunshe da bangarori daban daban kuma mai hada al'adu daban daban.

Kamar yadda shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya fada, birnin Shenzhen, sabon birni ne da JKS da jama'ar Sin suka gina bayan kasar ta yi gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, kuma wani birni ne na tsarin gurguzu mai halin musamman na kasar Sin da aka gina daga tushe. Jama'ar Shenzhen sun jure wahalhalu, sun yi gwagwarmaya, sun dauki shekaru 40 wajen gina wani birnin kasa da kasa, wanda zai dauki wasu kasashen waje shekaru 100 suna yin hakan. Wannan shi ne abin al'ajabi da jama'ar Sin suka samar da shi a tarihin ci gaban duniya.

Xi Jinping ya yi mana bayani kan yadda aka cimma wannan babbar nasara, ya ce, ruhin kirkire-kirkire, da zurfafa kwaskwarima, da bude kofa, da kuma tunanin mayar da moiyar al'ummar kasa a gaban kome, su ne sanadin cimma wannan babbar nasara.

Game da ruhin kirkire-kirkire, ya ce, birnin Shenzhen ya dukufa wajen 'yantar da karfin kawo albarka, da inganta bunkasuwar fasahohi, cikin ko wace shekara, ya zuba jarin kudin Sin yuan biliyan dari 1 a wannan fanni.

Game da batun gudanar ayyuka kuma, Xi ya ce, birnin Shenzhen yana kan gaba ta fuskar yin kwaskwarima ga tsarin tattalin arziki bisa bukatun kasuwannni, har ya fidda matakan kwaskwarima sama da dubu 1.

Game da bude kofa ga waje kuma, a shekarar 1980, karfin kudin shige da fice ya kai dalar Amurka miliyan 18, a shekarar 2019 kuma, adadin ya kai dalar Amurka biliyan 431.5, adadin da ya karu da kaso 26.1% a ko wace shekara. Kuma, akwai manyan kamfanoni guda 100 dake cikin jerin kamfanoni guda 500 dake kan gaba cikin duniya dake zuba jari a birnin Shenzhen.

Game da batun kula da al'umma kuma, Xi ya ce, a shekarar 2019, kudin da ko wane mutumin birnin ke iya kashewa ya kai yuan dubu 62.5, adadin da ya ninka sau 31.6 idan aka kwatanta da na shekarar 1985, lamarin da ya sa, al'ummomin birnin suka cimma burin gina zaman takewar al'umma mai matsakaicin wadata.

 

An shirya babban taron taya murnar cika shekaru 40 da kafa yankin tattalin arziki na musamman na Shenzhen a yau ranar 14 ga watan Oktoba.

Makomar birnin Shenzhen: Birnin zai kara bude kofarsa don maraba da kowa

A halin yanzu, tattalin arzikin duniya na fuskantar kalubaloli da yawa, wadanda kalubale sun kawo illa ga kasar Sin ma. Dangane da wannan yanayi, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ce, "Kar mu bari wadannan matsaloli su hana mu ci gaba, ya kamata mu nace ga wata daidaitaciyar turba, wato kara bude kofar kasarmu, da fito da wani nau'in tattalin arziki na duniya mai salon bude kofa ga kowa, da kafa kyakkyawar makoma ta bai daya, ga daukacin bil-Adam"

Don cimma wannan buri, shugaba Xi Jinping ya tsara wani cikakken shiri don taimakawa raya birnin Shenzhen, inda ya nuna yadda birnin zai kasance a nan gaba. Yanzu haka birnin zai samu karin damammaki na samu ci gaba a fannoni 8, wadanda za su zama dalilan da za su janyo hankalinka zuwa wannan birnin. Su ne:

Da farko, za a ci gaba da kokarin gudanar da ayyukan yankunan musamman na raya tattalin arziki, kuma za a rika kyautata su akai-akai. Sabon tsarin da za mu dauka wajen raya kasa, ba wani nau'in tsari ne na kulle kofa ba, maimakon haka za a kara bude kofa, da tabbatar da gudanar tattalin arziki a cikin gida, gami da kasuwannin kasa da kasa. Za a kuma fara da kafa wani sabon tsarin tattalin arziki mai salon bude kofa mai matukar inganci a birnin Shenzhen.

Na biyu, daya bayan daya, za a daidaita batutuwan da suka hada da samun aikin yi, da ilimi, da aikin jinya, da inshorar al'umma, da samun wuraren zama, da kula da tsoffi, da samar da abinci, da kare muhalli, da tsaron al'umma, da makamantansu. Za a yi kokarin tabbatar da cewa, jama'a za su samu karin kudin shiga, da jin dadin zaman rayuwa, tare da samun cikakken tsaro.

Na uku, shigo da wasu kwararrun kimiya da fasaha da kungiyoyin kirkire-kirkire da suka kan sahun gaba a duniya domin su taka rawa kan ci gaban birnin.

Na hudu, yin iyakacin kokarin fidda wata sabuwar hanya da ta dace da halayen birni mafi girma, ta yadda birnin zai bunkasa yadda ya kamata.

Na biyar, koyi daga fasaha mafi dacewa da zamani ta kasa da kasa, don kara karfin bunkasa sha'anin hada-hadar kudi, da nazari, da kuma tsai da shiri, da kuma fannin lissafin kudi da doka da shari'a, da dai sauran sha'anin ba da hidima na zamani.

Na shida, kokarin raya sha'anin kimiya da kirkire-kirkire da kafa sabbin masana'antu, ta yadda za a raya sha'anin sabon zamani da tattalin arzikin kasuwanci ta yanar gizo.

Na bakwai, kara hadin gwiwa da kasashen da suka shiga shawarar "Ziri daya da hanya daya" a duk fannoni.

Na takwas, tsayawa tsayin daka kan tsarin bude kofa dake neman amfanar juna, da cin moriya tare, ba kawai Sin ta samu karfin raya kanta daga duniya ba, har ma da yadda duniya za ta ci gajiyar bunkasuwar kasar Sin.

Shugaba Xi Jinping ya ruwaito wata waka dake cewa "Fure daya ba ya alamta zuwan lokacin damina, sai dai bayyanar furanni iri daban daban", inda ya bayyana cewa, da ba don wasu kasashe sun shiga an dama da su ba, da yankunan musamman na raya tattalin arziki na kasar, ba su samu irin ci gaban da suka samu cikin shekaru 40 da suka gabata ba.

Ya ce kasar Sin na maraba da shigar karin kasashe cikin manufarta ta yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare, da raya yankunanta na musamman na tattalin arziki, domin samar da wani sabon tsarin zurfafa tuntubar juna, da hada hannu wajen ba da gudunmawa, da kuma samun moriya tare.(Kande, Zainab, Tasallah, Maryam, Bello, Amina, Sanusi)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China