Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Taron shugabannin kungiyar G20 zai gudana ta kafar bidiyo daga ranar 21 zuwa 22 ga watan Nuwamba
2020-09-28 09:59:25        cri

 

Wata sanarwa daga Saudiyya, wadda ke shugabantar kungiyar G20 a wannan karo, ta ce taron shugabanninn kungiyar zai gudana ta kafar bidiyo daga ranar 21 zuwa 22 ga watan Nuwamba, karkashin jagorancin Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud na Saudiyyar.

Sanarwar ta ce a matsayinta na shugaba, Saudiyya za ta dora kan nasarorin da aka cimma yayin taron gama gari na shugabannin kungiyar da aka yi ta bidiyo a watan Maris da kuma sakamakon tarukan bidiyo sama da 100 na rukunoni da ministocin kasashen kungiyar.

Kungiyar G20 dake zaman katafaren dandalin hadin gwiwar tattalin arziki na duniya, na jagorantar yaki da annobar COVID-19, inda mambobin kungiyar suka bada gudunmawar sama da dala biliyan 21 domin tallafawa aikin samarwa da rabon kayayyakin lafiya da magunguna da riga kafin cutar.

Sanarwar ta ce yayin taron da aka yi wa taken "Gano damarmaki a karni na 21 ga kowa" shugabannin za su mayar da hankali kan kare rayuka da farfado da hanyoyin samun ci gaba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China