Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan noma da harkokin karkara na kasar Sin ya yi kira da a dage matakan kayyade fitar da hatsi
2020-09-14 11:22:19        cri
Ministan ma'aikatar noma da harkokin karkara na kasar Sin Han Changfu, ya yi kira da a dage matakan kayyade fitar da hatsi, da sauran muhimman nau'o'in amfanin gona. Han ya yi kiran ne yayin da yake jawabi ga mahalarta taron ministocin noma da albarkatun ruwa na kungitar G20 da ya gudana a ranar Asabar da ta gabata ta kafar bidiyo.

Ministan ya ce har yanzu cutar COVID-19 na kara yaduwa a sassan duniya, wanda hakan ke yin tasiri ga tsarin cinikayyar abinci, da isar sa sassa daban daban. Don haka akwai bukatar G20, a matsayin ta na kungiyar dake kunshe da kasashe mafiya karfi a fannin samar da amfanin gona a duniya, ta yi hadin gwiwa wajen tabbatar da an dakile kamfar abinci, tare da daidaito a wannan bangare.

Minista Han ya gabatar da wasu shawarwari guda hudu, wato bukatar hadin giwar samar da isasshen abinci a duniya. Da karfafa hadin gwiwar zuba jari da cinikayyar amfanin gona, da bukatar aiki tare wajen kawar da asara da barnata abinci.

Taron ministocin noma da albarkatun ruwa na kungitar G20, ya tattauna game da matakan shawo kan cutar CVID-19, da batun hadin gwiwa a bangaren zuba jari da cinikayyar amfanin gona, tare da nuna muhimmancin samar da daidaito a fannin noma, a gabar da ake fuskantar hadurra da kalubale masu nasaba da bullar annoba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China