Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
OECD: Cikin kasashe mambobin G20 kasar Sin ce kadai ta samu ci gaba a rubu'i na biyu na bana
2020-09-15 13:15:37        cri
Kungiyar bunkasa tattalin arziki da hadin gwiwa ta OECD, ta ce cikin daukacin kasashe mambobin kungiyar G20, kasar Sin ce kadai ta samu ci gaba a rubu'i na biyu na shekarar nan, a gabar da cutar COVID-19 ta yi mummunan tasiri ga harkokin tattalin arziki a rubu'i na farko na shekarar ta 2020.

Sanarwar da OECD ta fitar ta nuna cewa, Sin ta samu ci gaba na kaso 3.2 bisa dari a rubu'in na biyu cikin shekara guda, da kuma karin kaso 11.5 bisa dari a rubu'in da ya gabaci hakan.

Kaza lika matsakaiciyar raguwar wata wata da sauran kasashen kungiyar su 19 suka fuskanta, ta kai kaso 11.8 bisa dari. Kasar India ita ce ta yi asara mafi yawa, da kaso 25.2 bisa dari. Ita ma Amurka ta yi asarar kaso 9.1 bisa dari, yayin da karin wasu kasashen kungiyar 8 suka yi asarar sama da kaso 10 bisa dari.

Idan an hada da ci gaban da Sin ta samu a wannan fanni, kungiyar mai mambobi 20, ta samu raguwar GDP na kaso 6.9 bisa dari, a rubu'i na biyu na wannan shekara, idan an kwatanta da raguwar kaso 1.6 bisa dari da aka gani a rubu'i na farko na shekarar 2009, lokacin da duniya ta fuskanci komadar tattalin arziki. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China