Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilan kasashe masu tasowa na adawa da tsoma baki cikin harkokin kasar Sin da suka shafi HK da Xinjiang
2020-09-26 15:40:17        cri

Yayin wata muhawara a taron hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD karo na 45 da ya gudana a jiya, wakilan kasashen Myanmar da Koriya ta arewa da Cambodia da Laos da Madagascar da Venezuela da sauran wasu wakilai, sun bayyana goyon bayansu ga kasar Sin kan batutuwan da suka shafi HK da Xinjiang.

Wakilin kasar Myanmar ya ce, rashin adalci da siyasantar da batutuwa na tarnaki ga kokarin gwamnatocin kasashe masu tasowa na wareware batutuwan dake ci musu tuwo a kwarya, ciki har da yadda kasar Sin ke tunkarar matsalar ta'addanci da tsattsauran ra'ayi a jihar Xinjiang da kuma kokarin wanzar da zaman lafiya a yankinta na musamman na HK. Ya ce Myanmar na kira ga dukkan kasashe da kada su nemi yi wa hukumar kare hakkin dan Adam izgilanci bisa wasu batutuwa na siyasa.

A nasa bangaren, wakilin kasar Venezuela, ya bayyana adawa mai karfi ga zarge-zarge mara tushe da wasu daidaikun kasashe ke yi kan jihar Xinjiang ta kasar Sin.

Ya ce jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin, ta yi fama da barazanar ta'addanci da tsattsauran ra'ayi mai tsanani, kuma al'ummar jihar sun fuskanci matsalolin take musu hakkokinsu na rayuwa da kiwon lafiya da kuma ci gaba. Yana mai cewa gwamnatin jihar, ta yi kokarin shawo kan matsalar, kana tana da karfin kare al'ummarta.

Dangane da batun HK kuwa, ya ce gwamnatin yankin na kiyaye doka yayin da take tunkarar rikicin masu zanga-zanga. Kuma dokar tsaron kasa kan yankin na bisa doron doka, sannan ya dace wajen wanzar da zaman lafiya a yankin da kuma aiwatar da manufar "kasa daya mai tsarin mulkin biyu". (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China