2020-06-02 10:18:45 cri |
A cewar sanarwar, mista Trump ya sanarwa Putin tunaninsa game da gabatar da taron kolin G7 da yiwuwar gayyatar shugabannin Rasha, Australia, India da Koriya ta kudu.
Sun kuma tabo batun muhimmancin karfafa tattaunawa tsakanin kasashen biyu game da tsara dabarun tabbatar da zaman lafiya da gina ingantattun manufofi a fannin soji.
Bugu da kari, shugabannin kasashen sun tabo batun yadda za'a inganta kasuwar hada hadar danyen mai ta duniya ta hanyar aiwatar da yarjejeniyoyin kungiyar OPEC da sauran kasashen da ba sa cikin kungiyar. An bayyana cewa yarjejeniyar bangarori daban daban, wacce aka cimma tare da goyon bayan shugabannin kasashen Rasha da Amurka, za ta zama jagora wajen farfado da bukatun da ake da shi na danyen mai da kuma daidaita farashin mai a kasuwannin duniya.
A cewar sanarwar, Putin da Trump sun kuma tabo batun hadin gwiwa kan fasahar sararin samaniya da batun yaki da annobar COVID-19, inda suka amince za su ci gaba da tuntubar juna a matakai daban daban. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China