Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin a Amurka ya yi gargadi kan abubuwan dake neman lalata dangantakar kasashen biyu
2019-12-06 10:43:49        cri
Cui Tiankai, jakadan kasar Sin a Amurka ya ce a halin yanzu dangantakar Sin da Amurka tana cikin wani yanayi mai hadarin gaske, ya ce tilas ne su yi hattara game da masu kokarin neman rusa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta hanyar fakewa da takaddamar ciniki dake tsakaninsu.

"Tsananin neman karfin fada a ji, misali kamar kawo baraka, da sabon nau'in yakin cacar baka, da neman lalata tsarin wayewar kai, suna kara kunno kai", Cui ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a lokacin wani bikin liyafa wanda majalisar kula da harkokin ciniki ta Amurka da Sin suka shirya, wanda ya samu halartar wakilan kamfanonin Amurka sama da 200 wadanda ke huldar ciniki da kasar Sin.

Ya ce idan akwai yawan zargi, da nuna kiyayya, da neman kawo baraka, gami da yin fito-na-fito, idan za'a kyale wadannan abubuwa su ci gaba da kasancewa, to shin, wane iri sakamako ake tsakanin hakan zai iya haifarwa al'ummomin kasashen biyu har ma da duniya baki daya?.

Jakadan ya kara da cewa, kasar Sin tana kara lalibo hanyoyin ci gaba da yin aiki tare da bangaren Amurka domin kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen ta hanyar amincewar juna, da yin hadin gwiwa cikin lumana, domin cimma burinta na samun ingantaccen ci gaba mai dorewa. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China