Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin tana taka rawa a tsaron makamai masu guba a duniya
2019-12-04 10:02:37        cri
Babban jami'in diflomasiyyar kasar Sin ya ce a koda yaushe kasar Sin a shirye take ta goyi bayan yarjejeniyar tsaron makamai masu guba (BWC), kuma za ta ci gaba da taka mihimmiyar rawa game da harkokin tsaron makamai masu guba a matakan tsaron makamai masu guba na gwamnatoci a kasa da kasa.

A jawabin da ya gabatar a taron kasashe mambobin tsaron makamai masu guba na shekarar 2019 BWC, wanda aka bude a jiya Talata, Li Song, jakadan kasar Sin na sashen kawar da makaman nukiliya, ya ce, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a harkokin duniya don tabbatar da makoma mai kyau ga bil adama game da shirin tsaron makamai masu guba da kuma samar da alfanu ga jama'ar kasa da kasa domin al'ummar duniya su ci moriyar ci gaban kimiyya da fasahar zamani.

Kasar Sin za ta ci gaba da yin aiki tare da al'ummomin kasa da kasa domin inganta rayuwar dukkan bil adama, da tabbatar da inganci da martaba yarjejeniyoyi, da zurfafa hadin gwiwa da kasa da kasa game da tsaron makamai masu guba, da daga matsayin hadin gwiwar bangarori daban daban wajen takaita yaduwar makamai masu guba, da kuma gina al'ummar duniya mai kyakkyawar makoma ta hanyar tsaron makamai masu guba. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China