Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin da kasashe masu tasowa sun bayyana muhimmancin dangantakar kasa da kasa
2019-09-11 09:41:47        cri
Wakilin kasar Sin a MDD Chen Xu, ya ce a shirye kasar Sin da kasashe masu tasowa suke, su hada hannu da sauran kasashe wajen daukaka dangantakar kasa da kasa da mara baya ga tattaunawa da hadin gwiwa.

Da yake jawabi a madadin kungiyar kasashe masu tasowa, Chen Xu, shugaban tawagar kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva, ya bayyana yayin taro na 42 na hukumar kare hakkin dan Adam ta majalisar dake wakana cewa, la'akari da karuwar rashin tabbas da rashin tsaro a duniya, dangantakar kasa da kasa na da muhimmanci yanzu fiye da a baya.

Chen Xu na fatan hukumar ta kare hakkin dan Adam, za ta daukaka ka'idoji da burin MDD da gudanar da aiki mai ma'ana cikin adalci ba tare da bangaranci ba, da kuma adawa da siyasantar da ajandar kare hakkin dan Adam. (Faeza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China