Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan kasar Sin ya yi kira ga Amurka da Sin su hada gwiwa yayin da ake tsaka da fama da annobar COVID-19
2020-02-29 15:55:15        cri

Jakadan kasar Sin a Amurka, Cui Tiankai, ya yi kira ga Amurka da Sin, su hada hannu wajen magance kalubalen da duniya ke fuskanta. Yana mai gargadi game da yada jita-jita daga 'yan siyasa.

Cikin wata mukala da aka wallafa jiya a Amurka, Cui Tiankai ya ce tun bayan annobar COVID-19 a kasar, Sin ta yi namijin kokari wajen tunkarar cutar.

Ya ce a matsayinta na kasar da ta san ya kamata, Sin ta dauki managartan matakan hana yaduwar cutar a duniya. Yana mai cewa, ta yi ta fitar da bayanai masu alaka da cutar bisa gaskiya da sanin ya kamata.

Jakadan ya yi kira ga Sin da Amurka, kasashe biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, su hada hannu wajen shawo kan kalubale da matsalolin da duniya ke fuskanta bisa la'akari da al'ummomin kasashen biyu da na duniya baki daya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China