Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin tana sa ran hadin gwiwar kasa da kasa domin aiwatar da jadawalin neman dauwamammen ci gaba zuwa shekarar 2030
2020-09-25 21:07:23        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Jumma'a a birnin Beijing cewa, kasar Sin tana fatan yin hadin gwiwa da kasashen duniya, wajen karfafa ayyukan rage da kawar da talauci, da hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, da kuma aiwatar da jadawalin neman dauwamammen ci gaba zuwa shekarar 2030.

Ya kuma kara da cewa, shekarar bana shekara ce ta 75 da kafuwar MDD, kuma a ranar 26 ga wata, kasar Sin da hukumar tattalin arziki da zaman takewar al'umma ta MDD, da hukumar raya kasa da kasa ta MDD, za su kira taron tattaunawa game da kawar da talauci, da hadin gwiwar kasashe maso tasowa cikin hadin gwiwa.

Ana sa ran mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi zai jagoranci wannan taro. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China