Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta yi kira ga ofishin babban jami'in hakkin dan Adam na MDD da ya ci gaba da tuntubar kasashen duniya
2020-09-16 15:55:02        cri

Jiya Talata 15 ga wata, an yi babbar muhawara kan rahoton babban jami'in hakkin dan Adam na MDD, a yayin taro karo na 45 da kwamitin kula da hakkin dan Adam na MDD ya shirya, inda jakada Chen Xu, zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD a Geneva da kungiyoyin kasa da kasa a kasar Switzerland, ya yi jawabi a madadin kasashen da suke da ra'ayi kusan iri daya da na kasar Sin.

A cikin jawabinsa, Chen Xu ya ce, shekarar bara, shekara ce ta cikon shekaru 75 da kafuwar MDD. Don haka kamata ya yi kasashen duniya su rungumi duniya mai ba da damar cudanya tsakanin sassa daban daban, su inganta hadin kansu wajen daidaita kalubale tare.

Sakamakon barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, da matakin sanya takunkumi na kashin kai, ya sa wasu kasashe masu tasowa da kasashe mafiya rashin ci gaba suke fuskantar kalubale wajen kare hakkin dan Adam, don haka kasar Sin ta yi kira ga ofishin babban jami'in hakkin dan Adam na MDD, da ya bai wa kasashe masu ruwa da tsaki fasaha bisa bukatunsu, da kuma yin adawa da matakin sanya takunkumi na kashin kai. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China