Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta bukaci a kara himmantuwa da hada kai wajen yaki da ta'addanci da sauran laifuffuka
2020-08-07 10:56:37        cri
Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Zhang Jun, ya ce ya zama wajibi a kara himmantuwa tare da hada hannu a matakin kasa da kasa da yankuna, domin yaki da ta'addanci da laifuffuka.

Zhang Jun, ya shaidawa wani taron muhawara na kwamitin sulhu na MDD kan alakar ta'addanci da laifuffukan da ake shiryawa cewa, yayin da ta'addanci da aikata laifuffuka tsakanin kasa da kasa da sauran batutuwan tsaro a duniya ke karuwa da kara hadewa da juna, babu wata kasa dake da garkuwa daga wadannan kalubale na bai daya.

Ya ce kasar Sin na goyon bayan hadin gwiwa tsakanin hukumomin MDD, kamar ofishinta mai yaki da ta'addanci da kwamitin zartarwa mai yaki da ta'addanci da ofishin majalisar mai yaki da miyagun kwayoyi da laifuffuka da rundunar 'yan sandan kasa da kasa, da kuma hukumomin yankunan, domin hada karfi da karfi, bisa mabambantan manufofinsu.

Da yake tsokaci kan yadda ya kamata a yaki ta'addanci, jakadan ya ce dole ne a kiyaye ka'idojin MDD da martaba rawar da majalisar ke takawa wajen jagorantar ayyuka.

Ya kuma yi tsokaci kan inganta kwarewar jami'ai, yana mai cewa, abu ne mai muhimmanci taimakawa kokarin kasashe mambobin majalisar da kuma inganta karfinsu na magance kalubale. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China