Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi kira da a tsagaita bude wuta a duniya don yaki da annobar COVID-19
2020-09-10 13:45:19        cri
Jiya Laraba kwamitin sulhu na MDD ya kira wani taro kan annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta kafar Intanet, inda Geng Shuang, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya yi kira ga kasashen duniya, da su ci gaba da aiwatar da kudurin kwamitin mai lamba 2532, a kokarin tsagaita bude wuta a fannoni 4 don yaki da annobar cikin hadin gwiwa.

Da farko a dakatar da adawa da juna a kokarin shimfida zaman lafiya har abada. Na biyu, a nace ga martaba rayukan jama'a da kuma kara ba da tallafin jin kai. Na uku, a soke takunkumin kashin kai da wasu kasashe suka sanya, a kokarin rage wahalhalun da jama'a ke fuskanta. Na hudu, a tsagaita bude wuya tare da yaki da annobar, a kokarin kara azama kan samun zaman lafiya ta hanyar raya kasa.

Geng ya kara da cewa, shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya sanar a yayin babban taron lafiya ta duniya da aka shirya a watan Mayun bana cewa, za a mayar da allurar rigakafin annobar COVID-19 a matsayin kayan al'ummar kasa da kasa bayan da aka kammala nazari da kuma fara aiki da ita. Kasashen duniya da za su ci gajiyar allurar ta hanyoyi daban daban. Kuma dole ne a martaba manufar amfanawa dukkan bangarori kan batun allurar. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China