Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sakataren MDD ya yi kira da a kawo karshen rikicin siyasa a Lebanon
2020-09-24 12:08:04        cri

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, a ranar Laraba ya yi kira da a kawo karshe tirka-tirkar siyasar dake faruwa a kasar Lebanon, gami da aiwatar da gyare-gyare da suka wajaba.

Guterres ya ce, gabatar da sunan Mustapha Adib a matsayin firaministan kasar, abu ne da ya dace. Daga nan kuma, sai a kai ga kafa gwmnatin da za ta biya bukatu da ma muradun al'ummar kasar ta Lebanon, sai kuma a hanzarta aiwatar da muhimman sauye-sauye.

Ya ce, idan har ba a dauki irin wadannan matakai ba, to, kokarin da ake na sake gina kasar, zai bi ruwa, kari kan hargitsi da kuncin da al'ummar kasar ke fuskanta a halin yanzu. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China