2020-08-05 10:35:12 cri |
Gidan talabijin na al-Jadeed, ya ruwaito ministan na cewa, akwai yuwuwar sinadarin Ammonium nitrate da aka ajiye a wani dakin adana kayayyaki mai lamba 12 a tashar ruwan tun shekarar 2014 ne ya haifar da gobarar.
Ya ce za a tuhumi hukumomin kwastam game da dalilan da suka sanya aka adana sinadarai a tashar ruwan ta Beirut.
Ministan ya kuma tabbatar da cewa an shawo kan kaso 80 na gobarar da fashewar ta haifar.
Shugaban Lebanon Michel Aoun, ya kira wani taron gaggawa na majalisar tsaro domin tattauna musabbabi da abun da ya biyo bayan gobarar. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China