2020-08-05 10:01:42 cri |
Wata sanarwa da kakakin sa Farhan Haq ya fitar, ta ruwaito Antonio Guterres na jajantawa iyalai da al'umma da gwamnatin Lebanon, biyo bayan fashewar wani abu a birnin na Beirut a jiya. Inda ya yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki, ciki har da jami'an majalisar dake aiki a Lebanon.
Ya kara da cewa, MDD za ta ci gaba da ba Lebanon goyon baya a wannan muhimmin lokaci, kuma tana taimakawa wajen shawo kan lamarin.
Wasu abubuwa biyu da suka fashe sun girgiza birnin na Beirut a jiya Talata, lamarin da haddasa mutuwar mutane 50 tare da jikkata wasu 2,500.
Gobarar ta auku a tashar ruwa ta Beirut da misalin karfe 6:10 na yamma agogon kasar, inda ta girgiza gine-gine a fadin birnin da jikkata mutane tare da lalata abubuwa da dama. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China