Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasa da kasa sun yi alkawarin taimakawa Lebanon kan ibtilain abubuwan fashewa a kasar
2020-08-10 10:38:40        cri

Kasashen duniya sun yi alkawarin bayar da cikakken taimako kuma akan lokaci karkashin jagorancin MDD, domin taimakawa al'ummar kasar Lebanon wadanda mummunar fashewa ta yiwa illa a tashar ruwan birnin Beirut kwanaki biyar da suka gabata.

Bayan taron da aka gudanar ta kafar bidiyo wanda ya samu goyon bayan MDD, wanda shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya jagoranta, taron ya samu wakilcin kasashen Birtaniya, Qatar, Amurka, kungiyar tarayyar Turai, Sin, bankin duniya da sauransu, sun fitar da sanarwar hadin gwiwa inda suka yi alkawarin taimakawa al'ummar kasar Lebanon.

A cewar sanarwar, mahalarta taron sun yi alkawarin bayar da taimakon akan lokaci, kuma isasshen taimako, kana wanda ya dace da hakikanin bukatun mutanen kasar ta Lebanon, za'a gudanar da kyakkyawan tsari karkashin jagorancin MDD, kuma za'a bayar da taimakon ne kai tsaye zuwa ga mutanen kasar Lebanon, bisa ingantaccen tsari kuma ba tare da yin rufa-rufa ba.

Mataimakiyar babban sakataren MDD Amina Mohammed, ta fadawa taron cewa, domin taimakawa kasar Lebanon wajen kawo karshen wannan bala'i da kuma farfadowa daga tasirin bala'in, akwai bukatar dukkannin bangarori su hada hannu don yin aiki tare.

Amina Mohammed, ta bukaci a ba da fifiko kan muhimman bangarori hudu, wato bangaren kiwon lafiya, samar da abinci, gyara gine-ginen da suka lalace da kuma gyaran makarantu. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China