Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Lebanon: An fara fidda tsammanin samun masu rai yayin da ake ci gaba da aikin ceto
2020-08-10 11:17:09        cri
Masu aikin ceto a wajen da aka samu fashewa a yankin tashar jiragen ruwa a birnin Beirut, babban birnin kasar Lebanon, suna ci gaba da aikin ceton, sai dai an fara yanke tsammanin samun karin mutanen dake da sauran numfashi a wajen, sojojin kasar ne suka bayyana hakan a ranar 9 ga wata.

A lokacin taron karin haske kan ci gaban da aka samu game da aikin bincike da kuma aikin ceton da ma'aikatar tsaron kasar ke gudanarwa, rundunar sojojin kasar Lebanon ta sanar da cewa, bayan faruwar fashewar, tawagar aikin bincike da masu aikin ceto daga kasashen Faransa, Rasha, Qatar, Jamus, da sauran kasashe da suka je kasar ta Lebanon, sun gudanar da ayyukan bincike da aikin ceto a yankuna daban daban a wajen da aka samu fashewar. Bayan shafe tsawon kwanaki ana gudanar da aikin binciken da na ceton, babu wani cikakken fata da ake da shi na sake samun sauran mutane dake da numfashi a wajen.

Sakamaokn fashewar abubuwa da aka samu a yankin tashar jiragen ruwa a birnin Beirut da yammacin ranar 4 ga wata, ya sa kawo yanzu, mutane 158 sun mutu, sama da mutane 6000 sun samu raunuka sannan wasu gwamman mutanen sun bace. Bugu da kari, fashewar ta raba kimanin mutane dubu 300 da gidajensu. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China