![]() |
|
2020-09-24 12:03:26 cri |
Jiya ne majalisar dokokin kasar Somaliya, ta kada kuri'ar amincewa da sabon firaministan kasar da aka nada, Mohamed Hussein Roble, yayin wani zama na musamman da ta gudanar a Mogadishu, babban birnin kasar.
Da yake sanar da sakamakon kada kuri'ar, kakakin majalisar dokokin kasar Mohamed Mursal Abdirahman, ya ce baki dayan mambobin majalisar 215, sun amince da nadin Roble da shugaba kasar Mohamed Farmajo ya yi a makon da ya gabata.
A sakon da ya aikawa majalisar wakilan kasar, shugaba Farmajo, ya godewa 'yan majalisar saboda amincewa da sabon firaministan da ya nada, wanda zai kula da ayyukan gwamnati.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China