Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 16 sun mutu a sakamakon harin ta'addanci da aka kaiwa wani otel a Somaliya
2020-08-17 12:26:01        cri
An kai harin ta'addanci kan wani otel din dake kusa da bakin teku a Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya jiya Lahadi, wanda ya haddasa mutuwar mutane 16 ciki har da maharan, tare da raunatar mutane 28. A halin yanzu, sojojin kiyaye tsaron kasar sun riga sun killace wannan otel.

Kafofin watsa labaru na wurin sun rawaito kakakin gwamnatin kasar Somaliya Ismael Mukhtar Omar na cewa, dakarun al-Qaida guda 5 sun kai hari kan wannan otel a daren ranar 16 ga wata. Bayan dauki ba dai na tsawon awoyi fiye da 4, sojojin kiyaye tsaron kasar sun sake mamaye wannan otel. To sai dai kuma harin ya haddasa mutuwar fararen hula 10, tare da dan sanda daya, kana daya daga cikin dakarun 5 ya mutu a sakamakon fashewar bom, kuma an harbe sauran hudun har lahira.

Masu aikin ceto a wurin sun bayyana cewa, mutane a kalla 28 sun ji rauni a sakamakon harin. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China