Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu neman raba kasar Sin ba za su yi nasara ba
2020-08-19 20:38:34        cri
Yau Laraba, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a birnin Beijing cewa, jam'iyyar DPP ta yankin Taiwan tana neman raba kasa, amma, ba za ta cimma burinta ba, kuma gamayyar kasa da kasa ba za su goyi bayanta ba.

Rahotanni na nuna cewa, a ranar 18 ga wata, ma'aikatar harkokin waje da hadin gwiwar kasa da kasa ta gwamnatin tarayyar Somaliya ta fidda wata sanarwa, inda ta zargin yankin Taiwan cewar, yana neman bata 'yancin kai da cikakkun yankunan kasar Somaliya. Kafin haka kuma, akwai rahotanni dake nuna cewa, an bude karamin ofishin jakadancin yankin Taiwan na kasar Sin a Somaliland a hukumance.

Yankin Somaliland yana arewa maso yammacin jamhuriyar tarayyar kasar Somaliya, daya daga cikin yankuna masu cin gashin kansu na kasar Somaliya. A shekarun 1990s, yankin Somaliland ya sanar da 'yancin kansa, amma, bai samu amincewa daga gamayyar kasa da kasa ba. Gwamnatin kasar Somaliya tana mai da yankin Somaliland a matsayin wani bangaren kasarta, wanda ba za a iya raba shi daga kasar Somaliya ba. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China