Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO da UNICEF za su yiwa yaran Somaliya 400,000 rigakafin kyanda da shan inna
2020-09-01 12:51:04        cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO, da hukumar kula da kananan yara ta MDD UNICEF, sun fara wani gangami na yiwa yaran kasar Somaliya su 400,000 rigakafin kyanda da shan inna.

A jiya Litinin ne aka kaddamar da wannan gangami na kwanaki 3, wanda zai ba da damar yiwa yaran 'yan kasa da shekaru 5 alluran riga kafin. Kaza lika an tanaji jami'an lafiya 1,200, wanda za su baiwa yara sinadarin bitamin A, da magungunan kashe tsutsar ciki, a wasu wurare da aka tanada, duk kuwa da yanayi na fama da cutar COVID-19 da ake fuskanta, a gundumomi 17 na Banadir dake birnin Mogadishu.

Da yake tsokaci game da hakan, wakilin hukumar WHO a kasar Mamunur Malik, ya ja hankalin magidantan kasar, yana mai cewa dukkanin iyaye na da nauyin taimakawa yaran su, cimma nasarar kula da lafiya yadda ya kamata.

Jami'in ya ce karkashin wannan gangami, ma'aikatan lafiya za su tabbatar da bin ka'idojin hana yaduwar COVID-19, ciki hadda batun yawaita wanke hannaye, da sanya makarin fuska da safar hannu ta kariya, don kare lafiyar iyalai. Kana ma'aikatan za su rika musayar bayanai da iyalai don dakile yaduwar wannan cuta ta COVID-19. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China