Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jiragen saman kasa da kasa sun koma zirga-zirga a Somalia, watanni 4 bayan dakatar da su
2020-08-04 13:54:19        cri
Jiragen saman kasa da kasa, sun koma zirga-zirga a kasar Somalia a jiya Litinin, watanni hudu bayan tsaikon da aka samu saboda annobar COVID-19.

Hukumar kula da shige da fice ta kasar ta yi gargadin cewa, dole ne a kiyaye tsauraran matakan lafiya yayin da kasar ta bude sararin samaniyarta ga jiragen kasashen waje.

Hukumar ta ce ana bukatar shaidar gwajin cutar COVID-19 daga fasinjoji, kwanaki 3 kafin ranar tafiya, tana mai cewa hukumar za ta koma gudanar da ayyukanta a dukkan kafofin shiga kasar.

A cewar hukumar, dole ne matafiya su gabatar da shaidar dake tabbatar da cewa ba su da cutar COVID-19. Kuma ba a son takardar shaidar ta wuce sa'o'i 72 kafin lokacin tafiyar.

A ranar 30 ga watan Yuli ne, gwamnatin kasar ta sanar da cewa, jiragen kasashen waje za su koma aiki daga ranar Litinin, sannan ana sa ran bude makarantu da jami'o'i a ranar 15 ga wata, watanni 5 bayan rufe su da nufin dakile bazuwar COVID-19.

Gwamnatin ta kuma umarci hukumar shige da fice ta dauki matakan da suka dace na komawar tafiye-tafiye zuwa ketare.

Zuwa ranar Lahadi, an tabbatar da mutane 3,212 ne suka kamu da cutar a Somalia, inda 1,598 suka warke, yayin da cutar ta yi sanadin mutuwar mutane 93. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China