Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin kasar Somaliya sun hallaka 'yan bindiga bakwai a kudancin kasar
2020-09-17 10:08:59        cri
Rundunar tsaron kasar Somaliya, ta ce sojoji sun hallaka a kalla mayakan kungiyar Al-Shabab 7 tare da jikkata wasu da dama, yayin wani dauki ba dadi da 'yan ta'addan a garin Awdhigle, dake kudancin jihar Lower Shabelle.

Kwamandan runduna ta 66 Ahmed Maslah, ya bayyanawa manema labarai cewa, bayan arangamar sojoji da mayakan na Al-Shabab, sojojin sun kawar da wasu ababen fashewa da 'yan ta'addan suka dasa a hanyar Awdhigle. Maslah ya ce bayan cin lagon mayakan, sojoji sun shiga farautar su lokacin da suke kokarin buya a daji.

Yanzu dai dakarun tsaron gwamnatin Somaliya na kara kaimin daukar matakan soja, a wani yunkuri na ganin bayan mayakan Al-Shabab, dake ta da tarzoma a yankunan kudancin kasar. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China