Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi ya taya murnar bude ofishin jakadancin Sin dake kasar Solomon Islands
2020-09-21 13:52:45        cri
Yau Litinin, an bude ofishin jakadancin Sin dake kasar Solomon Islands。 A jawabin da ya gabatar yayin bikin bude ofishin, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana cewa, a ranar 21 ga watan Satumba na bara ne, kasashen biyu suka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu, matakin da ya bude sabon babin tarihin bunkasuwar dangantakar kasashen biyu.

A ranar 9 ga watan Oktoban shekarar bara, kwanaki 18 kacal da kasashen biyu suka kulla wannan dangantaka, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Solomon Islands Manasseh Sogavare a birnin Beijing, inda bangarorin biyu suka cimma matsaya daya kan bunkasa da zurfafa dangantakarsu. Hakan ya sa, kasashen biyu sun kara amincewa da juna a fannin siyasa da kara mu'ammala da hadin kai a fannoni daban-daban,. Haka kuma al'ummomin kasashen biyu sun kara fahimtar juna da dankon zumunci a tsakaninsu. Yayin da ake tsaka da yakar cutar COVID-19, kasashen biyu sun kuma taimakawa juna don a gudu tare a tsira tare, inda suka cimma nasara mai armashi.

Shugaba Xi Jinping ya ce, Sin na fatan kara hada kai da Solomon Islands da kuma yi amfani da wannan zarafi mai kyau na kafuwar ofishin jakadancin, don kara mu'amala tsakanin shugabanni ko jami'an sassan biyu, da habaka hadin kansu a duk fannoni, ta yadda za a zurfafa zumunci tsakanin jama'ar kasashen biyu da ingiza bunkasuwar dangantakar kasashen biyu, don amfanin jama'arsu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China