Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bukaci a samar da tsarin dokokin tsaron bayanai da kasashen duniya suka amince da su
2020-09-12 16:02:18        cri
Kasar Sin ta bukaci kasashen duniya dasu hada gwiwa wajen samar da dokokin tsaron bayanai wanda aka amince da shi a kasa da kasa, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi shi ne ya bayyana hakan a jiya Juma'a.

Wang yayi wannan tsokaci ne a lokacin da yake amsa tambayoyin 'yan jaridu game da shawarar da kasar Sin ta gabatar dangane da tsaron bayanai na kasa da kasa a lokacin taron manema labaru da aka gudanar tare da takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov.

Ya kara da cewa, shirin wanda Sin ta gabatar ya yi matukar jan hankalin duniya, Wang yace, kasashen duniya da dama sun bayyana shirin da cewar ingantacce ne kuma za su yi kyakkyawan nazari kansa.

An yi amanna cewa shawarar ta mayar da hankali kai tsaye game da batutuwan dake shafar al'amurran kasa da kasa, tare da neman mafita game da hanyoyin warware manyan matsalolin dake shafar batun tsaron bayanai daga dukkan fannoni.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China